GWAMNAN BAUCHI SANATA BALA YA SAMAR DA SHATALE TALE NA ZAMANI WANDA TA HADA HANYA UKU BAKARO,KAROFI, SHAGARI

KAN KUSURWAN FADA ROAD AND RANABOUT LINK BAKARO, KAROFI, SHAGARI 

Alhamdulillahi Muna Godiya wa Ubangiji daya nuna mana wannan Rana. Masha Allahu Godiya Maras Adadi wanda ya fito kai tsaye Daga Bakin Mutanen Wannan Unguwanni Guda Uku. Wannan Aikin Kamar Yadda Kuka Gani a cikin Hotuna ya nuni da cewa Aiki yazo Karshe Saura abu kalilan ne ya Rage Insha Allahu.

Kamar Yadda kowa yasani Cewa Bayan Dawowar Wannan Gwamnati na Biyu ta  Dukufa Wajen Wannan Aiki na wannan Guri. Wanda ta Hada Unguwanni guda Uku. Sanin kowane wannan Unguwanni Sune Unguwannin Farko a Jihar Bauchi.

Wannan Unguwa Tana Dauke da Tarihi da dama a Jihar Bauchi. Mai Girma Gwamna Sanata Bala Abdulkadir Muhammad CON, Kauran Bauchi, Jagaban Katagum, Turakin Ningi Yayi Alkwarin Sabunta wannan Unguwanni kuma Kowa ya Gani a Kasa.

Mai Girma Gwamna yayi Titi wanda ta tashi daga Kofar Gidan Alkali Aminu zuwa Bakaro ta wuce tudun yarima har ta zarce zuwa Kofar Dumi.Sannan yayi Hanya da Farkon Mashigar Hanyar Karofi Har zuwa Railway yadda ta Hade Unguwanni da dama a wannan yanki.

Mai Girma Gwamna ya Samar Da Sabon Titi wanda ta tashi daga Farkon Mashigar Hanyar Shagari Har Zuwa Kan Titin Railway. To Wadannan Hanya Guda Uku sune a yau Aka Hadesu Gaba daya Mashigarsu a Kan kusurwan Fada. Sannan Kuma Aka Samar Da Sha taletale na Zamani Domin Inganta wannan Guri. 

Al'ummar Mutanen wannan Yanki suna Godiya Wa Mai Girma Gwamna Sanata Bala Kuma suna cigaba da Buga kirji da alfahari cewa an cire musu kitse a wuta. Tabbas Wannan Abu Mai Girma Gwamna Bazai taba cirewa ba a zuciyar mutanen wannan Yanki. Mungode Mungode Mungode BABA KAURA .

Alh.Nuru Abdullahi (Baban Zarah)
Chairman Kaura Social Media Forum Bauchi State, Nigeria 
(KSMF-TV)

Popular posts from this blog

UNMASKING OMOYELE SOWORE'S HIDDEN AGENDA- BY SENIOR SPECIAL ASSISTANT FOR GOVEDNOR OFFI CE HON.SULEIMAN MUSA MAI POSTER

GOVERNMENT OF BAUCHI STATE HOLDS EDUCATION STAKEHOLDERS MEETING THE (SUBEB)