AN KORI MA'AIKACIN DAYA CINYE WA MMACI ALBASHINSA NA FANSHO NA WATANNI 55 A JIHAR BAUCHI. (KSMF-TV) REPORTERS BAUCHI STATE.

Gwamnatin jihar Bauchi Ta Kori Ma’aikacin Da Ya Cinye Wa Mamaci Fansho Watanni 55.

Hukumar kula da ma’aikata ta jihar Bauchi, ta samu tare da dakatar da izinin daukan aikin wani jami’i mai mukamin babban mataimain sakatare, Ibrahim Garba bisa samunsa da laifin kwashe watanni 55 ya na amsar fanshon wani mamaci, Abdu Mohammed.

Garba, wanda ma’aikacin gwamnatin jihar Bauchi da ke da ke aiki a karkashin hukumar kula da harkokin fansho, ya cinye naira miliyan N3, 017, 919.30 na marigayi Abdu Mohammed tun lokacin da iyalan Abdu suka kai rahoton cewa dan uwan nasu ya rasu.

“Ibrahim Garba ya amshi haramtaccen kudin fansho na watanni hamsin da biyar (55) da ya kai naira N54,871.26 kowace wata na tsawon shekaru hudu da watanni bakwai, sannan, adadin kudin da ya hamdame sun kai naira miliyan N3,017,919.30, kuma, kai tsaye za a kwatosu daga cikin hakkokinsa,” a cewar sanarwar da jami’in watsa labarai na hukumar kula da ma’aikata ta jihar Bauchi (BSCSC), Malam Saleh Umar ya fitar a ranar Talata.

Sanarwar ta kara da cewa: “Ibrahim Garba dai, kwamitin ladabtarwa na hukumar fansho ya sameshi hannu dumu-dumu da yin wasu ‘yan dabarbaru wajen sauya asusun ajiyar bankin Abdu Mohammed wanda ya rigamu gidan gaskiya (Mamaci) da asusun ajiyarsa da hakan ya ba shi damar canza maballen sirri bayan da ahlin mamacin suka kai masa rahoton rasuwar Malam ‘Abdu’”.

Saleh Umar ya kara da cewa, hukumar ta amince da kawo karshen aikin  Ibrahim Garba ne a yayin zamanta karo na 17 da aka gudanar a ranar 1 ga watan Agustan 2023.

“An samu jami’in da mummunar da’a ta hanyar shigar da kansa cikin badakalar albashi/fansho. Matakin nasa ya saba balo-balo wa tanade-tanaden dokokin aikin gwamnati (PSR) 0327(XI) da ta shafi almubazzarancin kudade.”

Kan wannan matakin shugaban hukumar kula da ma’aikata na jihar Bauchi, Alhaji Abubakar Usman Madakin Bunun Bauchi, ya yi kakkausar gargadi ga masu irin wannan dabi’a ko niyyar yin makamancin wannan da cewar su gaggauta sauya dabi’unsu domin a fadinsa yanzu ne ma aka sanya dabbar dakile hakan.

Shugaban ya ce, dole ne ma’aikata su kasance masu bin dokoki da ka’idojin aikin gwamnati domin tsarkakewa da tsaftace sashin aiki a kowani lokaci, ya na mai gargadin cewa duk wani ko wasu da aka kama da irin wannan ko makamancin wannan laifin tabbas zai fuskanci fushin hukumar ba makawa.

Ya bada tabbacin cewa, hukumar ba za ta zura ido tana kallo ko ta bari wasu bata-garin ma’aikata su kawo cikas ko bata kokarin gwamnati na kawo cigaba ga jihar musamman ta fuskacin kula da walwala da jin dadin aiki, sashin albashi da kuma biyan fansho.
 Alh.Nuru Abdullahi(Baban Zarah) Chairman Kaura Social Media Forum Bauchi State,Nigeria (KSMF-TV)

Popular posts from this blog

UNMASKING OMOYELE SOWORE'S HIDDEN AGENDA- BY SENIOR SPECIAL ASSISTANT FOR GOVEDNOR OFFI CE HON.SULEIMAN MUSA MAI POSTER

GOVERNMENT OF BAUCHI STATE HOLDS EDUCATION STAKEHOLDERS MEETING THE (SUBEB)