GWAMNAN JIHAR BAUCHI YAYI KIRA WA MAHAJJATA DASU CIGABA DA ADDU'O'I NA ALHERI WA SHUWAGABANNI NA NAJERIYA.
MAI GIRMA GWAMNA BALA YAJA HANKALIN ALHAZAN NAJERIYA DANA JIHAR BAUCHI DASUYI ADDUA WA SHUWAGABANNI.
Gwamna Bauchi Bala Ya Bayyana Hakan ne Yau wa Manema Labaru a Daga Kasa Mai Tsarki a Garin Minna Bayan An Gabatar da Jifa Na Karshe Yau Juma’a.
Gwamna Ya Kara Jan Hankali dasu sa tsoron Allah a Zukatansu Kuma Suyi Adalci a Tsakanin wa Juna Baki Daya a duk wasu Al’amuransu da Zasuyi da Junansu a Ko wani Lokaci.
Sannan Ya Kara Da Cewa INSHA Allah Kasar Najeriya Zata Farfado Daga Halin data Shiga. Sakamakon wash Tsare Tsare da Gwamnatin Tarayya takeyi da Kuma Gwamnatin Jihohi a Najeriya.
Sannan Kuma Yace Hakki ne a Kansu su samar wa Al’ummah Mafita mafi Saukin Rayuwa a Najeriya kasan cewarsu an Basu Jagoranci a Hanunsu. Don Haka Zasuyi iya Bakin kokarinsu suga Sun Sauke wannan Nauyi daya Rataya a Wuyarsu.
Daga Karshe Yace Insha Allahu Matasa da Mata Za’a Cigaba da Samar Musu abun dogaro dakai. Kuma Za’a Inganta Masana’antu da Sanya Jari Kuma a Samar da Masu Horadda Matasa domin su Koyi Sa’a ta Yadda Zasu Tsira da Mutuncinsu Dana Iyalansu.
Alh.Nuru Abdullahi(Baban Zarah)
Chairman Kaura Social Media Forum Bauchi State.