GWAMNAN BAUCHI BALA YA KAWO CIBIYAR HADA HADAR KASUWANCI A JIHAR BAUCHI KUMA SHINE OFFISHI NA FARKO A NAJERIYA:#KSMF REPORTERS BAUCHI STATE.

MAI GIRMA GWAMNA SANATA BALA DAN GARI YA SAKE KAWO MANA ALHERI A JIHAR BAUCHI.
   (#KSMF REPORTERS BAUCHI STATE)
            Rubutawa: Alh. Baban zarah.
 A satin daya wuce Babban Minista da Karamar Minista na Kasuwanci da Hada hadarta na Najeriya sun ziyarci Jihar Bauchi. Kuma wannan Ziyara taso shine Jihar Bauchi itace Jiha a Arewa Maso Gabas wanda tafi ko wace Jiha yin Hada Hada na Kasuwanci Lafiya da zaman lafiya da iyawa kana kuma da kulawa da kasuwancin yadda yadace cewar Babban Minista.

Babban Minista ya fara da Godiya wa Mai Girma Gwamna Bisa namijin kokari da yakeyi ma wannan Jiha ta ko wani Fanni a Jihar Bauchi. Sannan kuma Har kan kasuwanci ma yayi namijin kokari har sai da yaga Jihar Bauchi ta shigo a sawun Farko kuma tazo na Daya a Hada Hada a Najeriya.

Wannan Daliline yasa Suka zabi Jihar Bauchi a Matsayin Offishi na Farko a Najeriya wanda za’a Fara Hada,Hada Kai tsaye tun daga Kauyuka har zuwa Kasashe. Kuma nan Take suka karrama Mai Girma Gwamna a Matsayinsa na Gwamna daya kawo wannan Cigaba ma Jiharsa na Farko a Najeriya.

Mai Girma Gwamna yaji dadi matuka da wannan karamci na Zabar Jihar a matsayin na farko wanda za’a fara wannan Hada Hada kai tsaye ba tare da wata tangarda ba. wannan zamu kirashi da nesa ta matso kusa. Dama irin abunda ya dace kenan karamin dan kasuwa yayi kasuwanci cikin jin dadi kasuwancinsa ta kara bunkasa idan yanayi ne a Unguwarsu ya shigo dashi Jiharsu da Jihohi na Najeriya da Fita dashi kasashen waje.

Mai Girma Gwamna yace an Fara kafa wannan Offishine a Jihar Bauchi don ta taimaka wa yan’kasuwa na Gida da Sauran Yan’kasuwa. Kuma tuni aka bude wannan Sabon Offishi a Babban Sakateriya na Jihar Bauchi domin Fara gudanar da aiki tukuru.

Gwamnan yace Gwamnatinsa zata cigaba da bada duk abunda ya dace ma wannan Ma’aikata Kai Tsaye don Ganin a Nisa da wannan Hada Hada na Wannan cibiya dake shirin yi a Jihar Bauchi. 

Mai Girma Gwamna tuni ya zabi Shugaba a wannan Ma’aikata wanda shine (Coordinator na Jihar Bauchi) Dr. Bala Mahmood Abubakar kuma ya bada Umarni da duk abunda suke bukata suyi shi a rubuce su aiko masa domin ya samar da wannan abubuwa domin cigaba da wannan aiki a Jihar Bauchi.

Cikin Abubuwa da Mai Girma Gwamna yayi alkawarin badasu shine Samar da sabbin ma’aikata a wannan ma’aikata yadda ya bada umarni wa Shugaban ma’aikata daya bada su daga offishinsa sannan kuma samar musu motoci na wannan Ma’aikata domin cigaba da Gudanar da aiki.

Shima a nasa Dr. Bala Mahmood Abubakar din da wannan kafa mai albarka na #KSMF REPORTERS BAUCHI ta ziyarceshi ya nuna jin dadinsa matuka da abunda Mai Girma Gwaman yake musu tunda daga matakin farko Har aka kawo zuwa wannan Lokaci na bude wannan Offishi a Jihar Bauchi na cibiyar Hada Hadar Kasuwanci na Najeriya a Jihar Bauchi.

Kuma yace duk abubuwan da Mai Girma Gwamna yace a musu ana cigaba da yi musu kai tsaye tun daga Samar musu da Offishi da kayan cikin Offishin Sai kuma suna Jiran Ma’aikata da akace za’a turosu da kuma kudaden da zasu cigaba da gudanar da aikin tukuru. Sanan yace yasan saboda soyayya da Mai Girma Gwamna yakeyi na samuwar wannan Cibiya ya kara da cewa shi wannan guri tunda a sama yake akwai bukatar a samar da ruwa da wuri duk da ana titi a cikin wannan guri wanda yana ganin Kamar shi ya zuwan ruwan da wuta da kuma (Interlock ko tiles na zamani).

Kuma yace su a Shirye suke don Ganin sun Faranta wa Mai Girma Gwamna da Al’ummar Jihar Bauchi Rai Gaba daya. Dr. Bala yace aikinsu ba zai tsaya a iya offishi ba dole akwai tafiye tafiye da ziyaran kasuwanni don ganin yadda suke gabatar da kasuwanci yadda ya dace sannan kuma duk abunda suka ga ya dace da a fadadashi wato daga kasuwan kauye a fara safaransa zuwa wasu kasuwanni da suke kasarnan wannan cibiya zata dauki nauyi taga anyi wannan abu cikin sauki.

Dr. Bala Mahmood ya kara da cewa zasu shiga da fita a sauran kasashe domin su nuna musu muhimmancinsu domin suma su shigo don saka hajarsu a Jihar Bauchi don gudanar da kasuwanci cikin sauki a fadin Wannan Jiha na Bauchi.
        MUNGODE: Alh. Nuru Abdullahi (Baban zarah).

Popular posts from this blog

UNMASKING OMOYELE SOWORE'S HIDDEN AGENDA- BY SENIOR SPECIAL ASSISTANT FOR GOVEDNOR OFFI CE HON.SULEIMAN MUSA MAI POSTER

GOVERNMENT OF BAUCHI STATE HOLDS EDUCATION STAKEHOLDERS MEETING THE (SUBEB)