AYYUKAN DA MAI GIRMA GWAMNA BALA YAYI A JIHAR BAUCHI A BAYYANE SUKE MA KOWA:#KSMF REPORTERS BAUCHI STATE


 

Gajen haƙuri shi yake kawo me aka shuka inji ƴan Hausa.

Na fara da wannan matashiya ne don zayyana ayyuka na musamman da gwamnatin jihar Bauchi ƙarƙashin jagorancin Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad (Ƙauran Bauchi, Jagaban Katagum) ta samu nasarar gudanarwa.

Waɗannan ayyuka babu su cikin alƙawuran da me girma gwamna yayi a yaƙin neman zaɓen sa a shekarar 2019, an ƙirƙire su ne saboda buƙatar su da jihar Bauchi ke yi a wannan lokaci da kuma tasirin su wajen inganta rayuwar al'uma da kuma haɓaka tattalin arziki.

1. *LAFIYA*:
Ɗaga darajar wasu daga cikin manyan asibitocin ƙananan hukumomi, gina sabbin ɗakunan jinya da samar da kayan aiki na zamani da gadaje kafin, yayin da bayan ɓullar cutar murar mashaƙo na cikin ayyuka na musamman da Sanata Bala Muhammad ya samu nasara ƙirƙira da kammalawa.

Wannan ƙari ne ga kwaskwarima da gina sabbin ƙananan asibitoci (PHC) a dukkanin mazaɓun jihar Bauchi, sai kuma gina sabuwar shalkwatar ma'aikatar kula da inganta kiwon lafiya ta jiha.

Tarihi ba zai manta da aikin gwamnatin jam'iyyar PDP a jihar Bauchi ba kan gina babban asibitin Dambam da ɗaga darajar makwabcin sa na Misau la'akari da yawan al'umar yankunan a daidai lokacin da aka mayar da takwaran su na Alkaleri asibitin zamani, da kuma irin sa a Ɓagel, ƙaramar hukumar Dass.

Mu rufe da ɗakin gwajin cutuka na zamani da gwamnatin ta gina a asibitin kwararru na jiha wato Specialist.

2. *ILIMI*
Baya ga bayar da tallafin karatu ga ɗaliban jami'a da kwaleji, ginawa da kwaskwarima  wa ɗakunan karatu, Bala Muhammad ya samar da sauye-sauye na musamman don yi wa fannin ilimi garambawul.

Daga ciki akwai gina makaranti na musamman ga masu naƙasu da masu buƙata ta musamman da ma wasu makaranti a yankuna daban daban da aka kammala aikin gina su cikin makonni biyu ko ƙasa da haka.

Mu kammala da ɗaukar nauyin horas da ɗaruruwan ɗalibai kan sarrafa na'ura me kwakwalwa da kuma gudanar da mulki da haɗin guiwar cibiyoyi a birnin tarayya Habuja.

3. *NOMA* 
Ɗaukar nauyin horas da dubban matasan jihar Bauchi don koyon noma da kiwo na zamani a katafariyar gonar nan ta CS dake Lafiyan jihar Nassarawa, ba su jari da kayan gudanar da sana'oi na cikin ƙari daga ayyukan gwamnati na haɓaka sashen noma don wadata jihar Bauchi da abinci da kuma bunƙasa tattalin arzikin ta.

Sai kuma sake mara wa kamfanin samar da takin zamani na jiha don samar da sauƙi ga manoma da kuma yaƙi da zaman kashe wando.

Haɗa da baje-koli kayan amfanin gona da ƙananan sana'oin manoma mata da gwamnatin ke yi lokaci bayan lokaci.

4. *MUHALLI*
Aikin gina dubban gidaje masu rahusa a dukkanin shiyyoyin jihar Bauchi na daga cikin matakan faɗaɗa birane da inganta yankunan karkara da kuma rage cunkoson jama'a da gwamnatin ke yi.

Mu ƙara da samar da tagwayen hanyoyin shiga birni daga Durum  zuwa fadar jiha ta hanyar Kano da kuma Yuli zuwa kwaryar birni daga hanyar Maiduguri.

Sai kuma ruɓanya titin Dogon Yaro zuwa Otel din Zaranda, fitacciyar hanyar Sabon Ƙaura zuwa Miri da Ibrahim Baƙo zuwa Inkil da sauran ƙananan hanyoyin unguwanni.

Gyara da samar da sabbin motocin ɗibar shara ga hukumar kula da tsabtar muhalli ta jiha da samar da gyara fitillun tituna na cikin matakan gwamnati na tsaftace birane.

Waɗannan da sauran ayyukan da za mu zayyano a rubutu na gaba na cikin nasarorin da aka samu baya ga cika alƙawuran da aka ɗauka na wasu ayyuka a lokacin yaƙin neman zabe na shekarar 2019.


Popular posts from this blog

UNMASKING OMOYELE SOWORE'S HIDDEN AGENDA- BY SENIOR SPECIAL ASSISTANT FOR GOVEDNOR OFFI CE HON.SULEIMAN MUSA MAI POSTER

GOVERNMENT OF BAUCHI STATE HOLDS EDUCATION STAKEHOLDERS MEETING THE (SUBEB)