NIGERIAN HUNTERS AND FORESTRY SECURITY SERVICES TO SECURE FOREST IN THE STATE!#KSMF REPORTERS BAUCHI.
Mai Girma Gwamna Sanata Bala Kaura Yaba Shaidan aiki na wannan Mai'aikata domin cigaba da taimakawa tsaro a Jihar Bauchi da kuma taimaka wa dazuzzuka na Jihar Bauchi.
Wannan Offishi karkashin Jagorancin Alh.Umar Aliyu Shayi (S.S.A on Security Bauchi State) tuni ya Fara gudanar da wannan aiki. A cikin aikin da suka fara sun kama motoci guda 20 na itace da gawayi Wanda aka saresu ba'a bisa ka'idaba Wanda hakan ya saba wa doka.
Kuma tuni aka kafa kotu mai zaman kanta Wanda zata saurari kara kuma ta yanke hukunci nan take ma wadannan mutane.
Wannan kotu tayi aikintane a Offishin hunters na Jihar Bauchi dake kwanan Inkil anan Jihar Bauchi kuma tuni an gurfanar da mutane 15 kuma sun amsa laifinsu sannan kuma an yanke musu hukunci kai tsaye.
Shi a nasa Alh.Umar Aliyu Shayi yayi Magana yadda yace suna shiga lungu da sako domin kiyaye hakkonki al'umma Dana Gwamnati Sannan kuma yayi kira da mutane dasu bi ka'idah na Gwamnati wajen gudanar da hidimarsu sannan kuma yace a shirye yake ya tsare musu hakkinsu Don yana aikine domin Al'ummah.
Shima dai a masa Magatakarda na dindindin a ma'aikatar al'adu da yawaon Bude ido na Jihar ya yaba kwarai da wannan Abu da Gwamnatin Jiha tayi. Sannan kuma yayi kira wa Jama'a dasu guji aikata abunda ya saba wa doka a daji.