BARKA DA CIKA SHEKARA 52 A DUNIYA MAI MARTABA SARKIN BAUCHI DR.RILWANU SULEIMANU ADAMU:#KSMF REPORTERS BAUCHI)
Girmama masarautu da masu riƙe da sarautun gargajiya wajibi ne ga kowane ɗan ƙasa me kishin al'adun da muka gada iyaye da kakanni.
A yau me martaba Sarkin Bauchi, Sarkin Yaƙin Sarkin Musulmi, hadimin al'umar Bauchi kuma uban ƙasa Dakta Rilwanu Suleiman Adamu ke cika shekaru hamsin da biyu masu albarka a wannan duniya.
Sadaukarwa, ƙauna, son zaman lafiya da haɗin kai su ne tambarin me martaba, adalci kuma shi ne hatimin masarautar sa.