GWAMNAN JIHAR BAUCHI BALA YA BADA AIKIN HANYAR SANI ABACHA ROAD DAKE GARIN AZARE KUMA AIKI YAYI NISA!KSMF REPORTERS BAUCHI.


Gwamnatin Jihar Bauchi Karkashin Jagorancin Mai Girma Gwamnan Al'umar Jihar, His Excellency Distinguished Senator Bala Mohammed CON (Kauran Bauchi), Yanzu Haka Ta Na Gudanar Da Aikin Hanyar Unguwar Sani Abacha Da Ke Nan Cikin Kwaryar Garin Azare, Karamar Hukumar Katagum. 

Al'umar Unguwar Sani Abacha Dama Azare Baki Daya Sun Jima Su Na Nema Tare Da Mararin Ganin An Yi Mu Su Wannan Hanya Mai Matukar Muhimmanci, Saboda Muhimmancin Hanyar Musamman Wajen Zirga-Zirgan Al'uma Da Kuma Hada-Hadar Kasuwanci, Amma Ba Su Samu Ba Sai Yanzu A Lokacin Gwamnatin Mai Girma Kauran Bauchi. 

Da Hawan Sa Bisa Karagar Mulki, Saboda Kyautatawa Da Kuma Halin Dattaku Irin Na Sa, Tuni Mai Girma Kauran Bauchi Ya Dukufa Wajen Share Wa Wadannan Al'umomi Hawaye, Inda Yanzu Haka Ake Kan Aikin Wannan Hanya (Sani Abacha Road) Gadan-Gadan, Biyo Bayan Amincewa Da Kuma Ba Da Kwangilar Aikin Da Gwamnan Ya Yi, Inda Yanzu Haka Kamfanin Mother Cat Su Ke Gudanar Da Aikin Shimfid'a Wannan Hanya Kamar Yadda Za'a Iya Gani Cikin Hotunan Da Ke Kasa. 

Wani Abin Birgewan Kuma Shine; Wannan Hanya Mai Matukar Muhimmanci Da Kauran Bauchi Ke Shimfid'awa Za Ta Had'e Da Manyan Hanyoyi Guda Biyu Wadanda Suka Had'a Da:

*Sabon Bypass Na Maiduguri Da Kuma
*Hanyar Shira 

A Zantawar Da Muka Yi Da Al'umomin Wannan Unguwa Da Ma Sauran Al'umar Garin Azare A Yayin Ziyarar Duba Wannan Aiki, Sun Bayyana Farin Cikin Su Game Da Aikin Wannan Hanya (Sani Abacha Road) Da Mai Girma Kauran Bauchi Ke Yi Musu, Inda Suka Yi Masa Addu'o'i Na Alkhairi Tare Da Rokon Allah (SWT) Ya Maimaita Wannan Gwamnati Mai Tarin Albarka. 

Mai Girma Kauran Bauchi Be Yi Kasa A Gwiwa Wajen Ganin Ya Gina Sabuwar Jihar Bauchi Ba, Tun Bayan Da Al'umar Jihar Suka Fita Kwansu Da Kwarkwata Suka Zabe Shi Da Dubban Kuri'un Su A Matsayin Gwamna.

Mun Gaishe Da Gwamnan Fita Kunya. 

Isah Lukman Azare 
Zonal Coordinator (Bauchi North) 
KAURA Social Media Forum 
August 10, 2022

Popular posts from this blog

UNMASKING OMOYELE SOWORE'S HIDDEN AGENDA- BY SENIOR SPECIAL ASSISTANT FOR GOVEDNOR OFFI CE HON.SULEIMAN MUSA MAI POSTER

GOVERNMENT OF BAUCHI STATE HOLDS EDUCATION STAKEHOLDERS MEETING THE (SUBEB)