BABBAN ALBISHIR: KAURAN BAUCHI YA AMINCE DA BADA AIKIN GINA SABBIN HANYOYI A KANANAN HUKUMOMIN KATAGUM DA ZAKI
Isah Lukman Azare ✍️
A Ci Gaba Da Canja Fasalin Jihar Bauchi Da Gwamnatin Sa Ke Yi, Cikin Ikon Allah Mai Girma Kauran Bauchi Ya Amince Tare Da Bayar Da Umarnin Aikin Sabbin Hanyoyi Har Guda Uku (3), A Kananan Hukumomin Katagum Da Kuma Zaki.
Sabbin Hanyoyin Da Kauran Bauchi Ya Amince Da Ginawa Sune Kamar Haka:-
1- Hanyar Madangala Zuwa Kujuru, Wacce Za Ta Tashi Tun Daga Garin Madangala Har Zuwa Garin Kujuru Duk A Yankin Karamar Hukumar Katagum.
2- Hanyar Unguwar Sani Abacha (Sani Abacha Road) Unguwar State Low-Cost, Azare.
3- Titin Garin Bakari Zuwa Kafin Larabawa A Karamar Hukumar Zaki.
Shakka Babu, Mai Girma His Excellency Distinguished Senator Bala Mohammed CON (Kauran Bauchi) Ya Faranta Kana Ya Kyautatawa Al'umomin Wadannan Yankuna, Duba Da Yadda Wadannan Hanyoyi Za Su Taka Muhimmiyar Rawa A Cikin Rayuwar Su, Musamman Wajen Samun Saukin Zirga-Zirga, Sufuri Da Kuma Hada-Hadar Kasuwanci.
A Madadin Al'umar Wadannan Kananan Hukumomi Guda Biyu Dama Shiyyar Arewacin Bauchi Baki Daya, Muna Amfani Da Wannan Dama Wajen Mika Sakon Godiyar Mu Marar Misaltuwa Ga Mai Girma Kauran Bauchi Bisa Amincewa Da Gina Mana Wadannan Gagara-Badau Din Hanyoyi Da Yayi.
Mun Gaishe Da Gwamnan Fita Kunya.
Isah Lukman Azare
KAURA Social Media Forum
June 9, 2022