JARIDAR LEADERSHIP TA KARRAMA GWAMNAN BAUCHI BALA A MATSAYIN GWARZON SHEKARA!#KSMF REPORTERS BAUCHI....



Jaridar Leadership ta karrama Gwamnan Jihar Bauchi Mai Girma Sanata Bala Abdulkadir Mohammed a matsayin Gwarzon Gwamnan Shekara saboda kwazon da ya nuna wajen tabbatar da zaman lafiya a Jihar Bauchi baya ga bullo da tsare-tsare da nufin tabbatar da tsaro an karewa tare da inganta rayuwar ‘yan jiha

Da yake jawabi yayin bikin da aka gudanar a babban dakin taron kasa da kasa na ICC a Abuja Bala Mohammed wanda ya sadaukar da kyautar ga ‘yan jihar Bauchi ya ce hakan zai kara masa kwarin gwiwa wajen kara yi wa ‘yan Najeriya karin fahimtar kalubale da bambance-bambancen dake tattare da wannan jiha mafi yawan al’umma a Afirka.

A cewar Bala Mohammed gwamnatin sa ta samar da matakan magance matsalar rashin zaman lafiya da rashin tsaro baya ga aiwatar da ayyukan raya kasa da dama duk kuwa da kalubalen tattalin arziki da ake fama da shi ya kara da cewa duk nasarorin da gwamnatinsa ta samu ta samu ne sakamakon goyon baya da kalaman karfafa gwiwa daga sarakunan gargajiya, dattawa,masu ruwa da tsaki dakuma al ummar wannan jiha. 

Yayin da yake yabawa shuwagabanni da ma’aikatan jaridar Leadership,Bala Mohammed ya ce karramawar za ta taimaka matuka wajen kara masa kwarin gwiwa da kokarin samarwa‘yan Jihar Bauchi dama Najeriya kyakkyawan shugabanci da suke bukata.

Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osibanjo da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da Muhammadu Inuwa Yahaya da Fayemi Kayode na Sokoto da Gombe da Ekiti da sauran wadanda suka halarci taron sun taya Gwamna Bala murna tare da yin kira gare shi da ya kara himma wajen gudanar hidimominsa

Jallah katemaki gwamnatin kaura. 

I'm Habibu Tubeela Azare
Kaura social media forum.

Popular posts from this blog

UNMASKING OMOYELE SOWORE'S HIDDEN AGENDA- BY SENIOR SPECIAL ASSISTANT FOR GOVEDNOR OFFI CE HON.SULEIMAN MUSA MAI POSTER

GOVERNMENT OF BAUCHI STATE HOLDS EDUCATION STAKEHOLDERS MEETING THE (SUBEB)