GWAMNA BAUCHI BALA YA SABUNTA FADAR HAKIMIN ITAS!#KSMF REPORTERS BAUCHI.
Isah Lukman Azare ✍️
A Kokarin Gwamnatin Sa Na Inganta Fannin Masarautun Gargajiya A Fadin Jihar Bauchi, Mai Girma His Excellency Distinguished Senator Bala Mohammed CON (Kauran Bauchi), Yanzu Haka Ya Na Kan Aikin Sabuntawa Da Kuma Canja Fasalin Fadar Mai Girma Hakimin Itas, Tafidan Katagum, Alhaji Sagir Abdullahi.
Kamar Yadda Ake Iya Gani Cikin Hotunan Dake Kasa, Aikin Sabunta Wannan Fada Mai Matukar Muhimmanci Ya Yi Nisa, Kana Ya Na Gudana Cikin Inganci.
Tun Bayan Hawan Sa Bisa Karagar Mulki A Shekarar 2019, Mai Girma Kauran Bauchi Bai Yi Kasa A Gwiwa Wajen Ganin Ya Gina Sabuwar Jihar Bauchi Ba, Inda Gwamnan Ya Dukufa Wajen Shimfid'a Ayyukan Alkhairai A Birni Da Karkara Na Jihar.
Mun Gaishe Da Gwamnan Fita Kunya.
Isah Lukman Azare an Baban Zarah!
KAURA Social Media Forum
May 10, 2022!