DAN'TAKARAN SHUGABAN KASA A KARKASHIN JAM'IYAR PDP KUMA GWAMNA BAUCHI YA ZIYARCI MASU TSAIDA DAN'TAKARA NA JIHOHIN ENUGU DA ANAMBRA DA EBONYI!#KSMF REPORTERS BAUCHI.
Isah Lukman Azare an Baban Zarah✍️
A Cigaba Da Zagayawa Zuwa Jihohin Kasar Nan Da Ya Ke Yi Domin Ganawa Da Masu Ruwa Da Tsaki Da Kuma Delegates Na Jam'iyyar PDP Domin Neman Goyon Bayan Su, Cikin Ikon Allah Yau Talata, Mai Girma Gwamnan Al'umar Jihar Bauchi, Kana Daya Daga Cikin 'Yan Takarar Shugabancin Kasa, Mai Girma His Excellency Distinguished Senator Bala Mohammed CON (Kauran Bauchi) Ya Ziyarci Jihohin Anambra, Ebonyi Da Kuma Enugu.
A Yayin Wannan Ziyara Wacce Ya Gana Da Masu Ruwa Da Tsaki Da Kuma Masu Zaben Dan Takara (Delegates) Na Jihohin Uku (3), Mai Girma Kauran Bauchi Ya Kara Bayyana Musu Aniyar Sa Ta Neman Sahalewar Jam'iyyar Wajen Tsayar Da Shi Takarar Shugaban Kasa, Da Kuma Irin Kudirce-Kudirce Na Alkhairi Da Yake Da Shi Game Da Nigaria Dama Al'umar Kasar Baki Daya.
Irin Tarba Ta Musamman Da Kauran Bauchi Ya Ke Samu A Dukkanin Ziyarar Da Yake Kayiwa Zuwa Jihohin Kasar Nan, Hakam Ya Ke Kara Tabbatar Mana Cewa; Tabbas Wannan Tafiya Akwai Alkhairi Cikin Ta.
Muna Addu'ar Allah (SWT) Ya Zama Mana Jagora A Kan Wannan Al'amari Na Ci Gaban Kasa Da Mu Ka Sa Gaba, Ya Kuma Arzuta Nigeria Da Samun Kauran Bauchi A Matsayin Shugaba A 2023.