DAN TAKARAN SHUGABAN KASA KARKASHIN JAM'IYAR PDP MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR BAUCHI YA GANA DA MASU TSAIDA DAN'TAKARA A MATAKIN JAM'IYA (DELEGATES) NA GARIN JIGAWA!#KSMF REPORTERS BAUCHI.



Gwamnan Jihar Bauchi kuma daya daga cikin masu neman takarar shugabancin Kasar nan a zaben da za'a gudanar ranar 28 da 29 ga watan Mayu 2022, H.E. Sanata Bala Abdulkadir Mohammed CON. 

A jawabinsa ya bayyana rawar da jagoran talakawa Dr. Sule Lamido CON suka yi wajen tabbatuwar Kasar nan da Jam'iyyar PDP shine yasa har suka samu wajen fitowa domin su bada gudunmawarsu a Kasar

Ya bayyana irin rawar da ya taka a ministan Abuja da aiyyuka da yayi a waje daban- daban da cewar yayi su ne domin inganta rayuwar mutane, a zamansa gwamnan Jihar Bauchi yayi aiyyuka na musamman da kowa yake amfana. 

Ya bayyana takararsa da cewar takara ce ta inganta rayuwar mutanen karkara, birni da kowanne lungu da Sako. 

Shugaban Jam'iyyar PDP na Jiha Dr. Babandi Ibrahim ya bayyana ziyarar da cewar ziyara ce ta yan gida ga yayansu kuma tarayya ce ta zumunci me karfi da aka dade dashi, ya bayyana Gwamna Bala da cewar yana da dukkan cancanta kuma yan Jigawa suna yi masa fatan alheri a wannan zabe. 

Allah ya bawa Jam'iyyar PDP dukkan nasarar a 2023.

Popular posts from this blog

UNMASKING OMOYELE SOWORE'S HIDDEN AGENDA- BY SENIOR SPECIAL ASSISTANT FOR GOVEDNOR OFFI CE HON.SULEIMAN MUSA MAI POSTER

GOVERNMENT OF BAUCHI STATE HOLDS EDUCATION STAKEHOLDERS MEETING THE (SUBEB)