WATA GIDAN JARIDA A NIGERIA MAI SUNA (SUN NEWPAPER) TA KARRAMA MAI GIRMA GWAMNA BAUCHI BALA A MATSAYIN GWARZON SHEKARA 2021!#KSMF REPORTERS BAUCHI.....
Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya karbi takardar tsayawa takarar shugaban cin kasar Najeriya ta hannun Hukumar Kamfanin Sun Publishing Limited din.
Da yake jawabi a lokacin gabatar da taron a gidan gwamnatin Bauchi, Gwamna Bala ya nuna jin dadinsa ga ‘yan jaridun da suka same shi da ya cancanci karramawar, inda ya bayyana hakan a matsayin kara karfafa masa gwiwa.
Yace karramawar da takwarorinsa a harkar yada labarai suka yi masa za ta ci gaba da zaburar da shi wajen kara himma ga al’ummar mazabarsa da kuma tabbatar da martabar sana’ar da kuma mutunta'ta
Gwamnan ya yabawa jaridar Sun saboda kwarewa da kuma sha'awar cigabansa sannan ya yi alkawarin mayar da martani wannan matakin don amfanin 'yan Najeriya.
A cewar Bala Mohammed,a matsayinsa na ‘dan jarida, yana da dukkan abubuwan da ya kamata, kuma ya shirya tsaf don gudanar da duk wani aiki na kasa,kuma ya ba da tabbacin inganta rayuwar ‘yan kasa shi ne babban abin da ya sa a gaba.
Gwamna Bala ya kasance yana mika godiyar sa ga kungiyar dattawan Arewa bisa yadda suka amince da shi a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP na yankin Arewa maso Gabas tare da godewa magoya bayansa bisa hadin kan da suka ba shi kan burinsa.
Tun da farko,Manajan Darakta na Sun Publishing Limited, ya ce an zabi Gwamna Bala ne bisa la’akari da irin ayyukan da ya yi da kuma nasarorin da ya samu tun hawansa kujerar Gwamnan Jihar Bauchi da kuma kokarin aiwatar da tsare-tsaren sa na ci gaban Jihar Bauchi.
Ya yabawa Gwamnan bisa gagarumin nasarorin da ya samu ta fannin kiwon lafiya, ilimi, gina hanyoyi,inganta rayuwar mata da matasa, samar da gidaje da dai sauransu,ya kuma bukace shi da kada ya yi kasa a gwiwa wajen yi wa kasa hidima.
Jallah katemaki gwamnatin kaura
i'm Habibu Tubeela Azare