MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR BAUCHI YA KARBI BAKUNCIN JAMI'AN UNICEF NA KASA KARKASHIN RESHEN JIHAR BAUCHI A GIDAN GWAMNATIN JIHAR BAUCHI!#KSMF REPORTERS BAUCHI....



Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed Kaura ya karbi bakuncin jami'an ofishin UNICEF a jihar Bauchi. 

Gwamna Bala wanda ya yi maraba da shirye-shirye daban-daban da hukumar UNICEF ke aiwatarwa a Bauchi, ya kuma ba su tabbacin a shirye yake ya yaba da kokarin da suke yi na ci gaban harkokin kiwon lafiya. 

Ya ce yarjejeniyar fahimtar juna da gwamnatinsa ta sanya wa hannu tare da UNICEF zai taimaka wajen samar da ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar jihar. 

Ya yabawa dukkanin abokan huldar ci gaban da suka shahara daga cikinsu sun hada da UNICEF, WHO, Aliko Dangote, Bill da Melinda Gates bisa alkawuran da suka dauka.

Gwamna Bala ya umurci hukumomin kiwon lafiya a jihar da su tabbatar da aiwatar da shirye-shirye masu inganci kan harkokin kiwon lafiya domin inganta harkar rigakafi. 

Tun da farko, shugaban ofishin UNICEF na Bauchi, Mista Tushar Rane ya taya Gwamna Bala murna kan dimbin nasarorin da gwamnatinsa ta samu a fannin kiwon lafiya ya kara da cewa jihar Bauchi ce jiha ce ta UNICEF a kan gaba a sakamakon ayyukan da Gwamna Bala Mohammed ya yi. Allah ya taimaki Mai Girma Gwamna akan ayyukansa na Alheri......Muna Godiya a Jihar Bauchi.

Popular posts from this blog

UNMASKING OMOYELE SOWORE'S HIDDEN AGENDA- BY SENIOR SPECIAL ASSISTANT FOR GOVEDNOR OFFI CE HON.SULEIMAN MUSA MAI POSTER

GOVERNMENT OF BAUCHI STATE HOLDS EDUCATION STAKEHOLDERS MEETING THE (SUBEB)