GWAMNAN BAUCHI SANATA BALA YA HALARCI RUFE TASFIRIN AL'QUR'ANI MAI GIRMA NA BANA A MASALLACIN GWALLAGA DAKE GARIN BAUCHI!#KSMF REPORTERS BAUCHI....
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Abdulƙadir ya halarci rufe tafsirin Alƙur'ani me girma a masallacin Jumu'a na Gwallaga, fadar jihar Bauchi.
Da yake jawabi, Gwamna Bala kira yayi ga al'uma musulmi da su yi aiki da darussan da suka koya cikin tafsirin littafin Allah maɗaukakin Sarki.
Gwamna Muhammad sai yayi amfani da damar wajen yabawa shahararren malamin addinin Islama, Sheik Sani Umar Rijiyar Lemu kan gudummawar da yake bayarwa wajen yaɗa addinin musulunci, inganta haɗin kai da zaman lafiya.
Gwamna Bala Muhammadbya ƙara da cewa dukkanin shirye-shiryen gina cibiyar yaɗa addinin musulunci a jihar Bauchi, wacce za'a sanyawa sunan fitaccen malamin sun kammala.
Shima a nasa jawabin, Sheik Farfesa Rijiyar Lemu taya gwamnan murnar gina masallatai da makarantin Islamiyya baya ga romon dimokraɗiyya kana yayi kira ga al'umar jiha da su cigaba da mara masa baya don kai ga nasara.