AIKIN SABUNTA TITIN YAKUBU/WANKA DAKE GUNDUMAR DAWAKI YANA CIGABA DA GUDANA!#KSMF REPORTERS BAUCHI.
By: Baban Zarah.
Cigaba da Aikin Hanyar wanda Ta-taso Daga Bakin kasuwa Central Market zuwa yakubu wanka har Abubakar Tabawa Balewa Estate dake nan Cikin Garin Bauchi. Aiki akeyi babu kama kafar yaro ko ina ya chanza sufa.
An Sabunta wannan Hanya ne Saboda tayi Dai-dai Da Zamani. Domin Al'ummar Wannan yanki Suma su amfana da Romon Dimokradiyya na Gwamanatin Maigirma Gwamna Sen. Bala Abdulkadir Muhammad.
Hakika lokacin da mukazo neman kuri'unku munce ku bamu kuma zamu muku abunda ya dace kuma zamu farfado da Jihar Bauchi kuma Alhamdulillahi Gaskiya kwalliya tana biyan kudin sabulu..
Daga Karshe muna shaida muku cewa da izzinin Ubangiji duk ayyukan da muka fara zamu gama hakazalika wanda muka gadama mun gama. Sannan kuma zamu cigaba da bude Jihar Bauchi domin mu rage cinkoso kana kuma mu gyara magudanan ruwa komai ya dace da zamanin da muke ciki.
Alhamdulillahi yau idan ka jima bakazo Bauchi ba ka shiga wasu Unguwanni a Jihar Bauchi zakace ba Bauchi bane sakamakon yadda Mai Girma Gwamna Sanata Bala Kaura yake kan gyara Jihar Bauchi Gaba Daya..
Mungode BABA KAURA GO FOR 8 Insha Allahu...