AIKIN HANYA WANDA TA TASHI DAGA TORO-RIMI-TULAI-PALAMA ZUWA DASS YAYI NISA KAMAR YADDA GWAMNATIN SANATA BALA TAYI ALKAWARI!#KSMF REPORTERS BAUCHI.
By: Baban Zarah.
Mai Girma Gwamna Jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed yayi alkawarin samarda hanyar da zata hada ƙananan hukumomin Toro da Dass, yayin da yaje ziyarar duba aiki a shekarar bara a ƙaramar hukumar Dass.
Maigirma gwabnan yabada aikin hanyar data tashi daga Dass wanda zata bulla har garin Rimin Zayam na karamar hukumar Toro dake wannan jiha.
Hanyar wanda zai taimaka wa manoma da yan kasuwa daga ƙananan hukumomin biyu, wanda zai shafi kauyukan da suke kan hanya, wanda yataso Daga Toro, Rimi, Tulai, Palama, Dass.
Ana cigaba da aikin wannan hanya yanzu haka,Kamar yadda Mai Girma Gwamnan Bauchi yayi Alkawari.Wannan Hanya ta jima tana ciwa Mai Girma Gwamna tuwo a kwarya Hakanne yasa yace Insha Allahu zai samar da Wannan Hanya Saboda sake Fadada Wannan Karamar Hukumomi Guda Kuma Hakan zai samar da Rayuwa mai inganci a Kauyukan da suke cikin Lungu na wadannan Kananan Hukumomi Guda Biyu.
Fatanmu shine Kamar Yadda Mai Girma Gwamna Sanata Bala ya dauki Alkawari a fadin Jihar Bauchi, Ubangiji ya cigaba da bashi Gudunmuwa ya kara masa budi da Hanyoyin shiga na Kudi domin cigaba da Fadada Jiharmu ta Bauchi...Mungode