MAI KAMA DA ZUWA SHI AKE AIKA HON.SULEIMAN MUSA MAI POSTER YA AMSA KIRA 2023 DAN MAJALISA NA CIKIN GARI!!! #KSMF REPORTES BAUCHI.

Assalamu Alaikum yan'uwana Barkanmu da safiya ubangiji ka bamu nasara akan dukkanin abunda muka saka a gaba ya gafarta mana zunu banmu..

 Da farko zan farane da taya murna wa Shugaban wannan gida kuma mai gidanmu a siyasa WATO HON.SULEIMAN MUSA MAI POSTER AMANA GWAMNA murnan sayan form na tsayawa takara da yayi jiya a Babban birnin tarayya Abuja.

Hakika wannan ya nuna mazantakarsa da Jajircewarsa da kuma takaici da yakeji ma al'ummarsa bisa koma baya da suka samu na cin moriyan dimokradiya shiyasa ya amsa wannan kira kuma yaje tuni ya yanki form don tsayawa takara DAN MAJALISAN JIHA BAUCHI CIKIN GARI.

Sanin kune wannan shine karo na biyu da wannan bawan Allah ya sayi form ya saya a 2019 amma baiyi ikonsa ba sannan kuma ya sake saya yanzu kuma Insha Allahu a wannan karo muna masa kyakykyawan zato da tsammani duba da halinsa da Dattakonsa da kuma yadda ya rike al'ummarsa musamman Mata da Matasa.

 Sunan wannan bawan Allah ba'a boye yake ba sannan kuma duk ayyukansa a fili yake da taimakonsa duk a bayyane yake baya buya kamar yadda sauran yan'siyasa sukeyi...

 Don haka muna kara kira da Babban murya cewa mutanen Bauchi cikin Gari kakarmu ta yanke saka domin kuwa dan'mu ya fito kuma ya amsa kira fatan shine kuyi masa addu'an alheri.

Daga karshe muna godiya wa al'ummah tun daga wadanda sukayi masa addu'a da kuma wanda suka rakashi wajen sayan form nasa da kuma wadanda sukayi dawainiya Ubangiji ya saka da Alheri sannan ku sani wannan abu duka namune don haka mu zage damtse mu cigaba da gayawa Allah musamman ga Azumi ya karato...Mungode: BBzarah (#KSMF REPORTERS BAUCHI)

Popular posts from this blog

UNMASKING OMOYELE SOWORE'S HIDDEN AGENDA- BY SENIOR SPECIAL ASSISTANT FOR GOVEDNOR OFFI CE HON.SULEIMAN MUSA MAI POSTER

GOVERNMENT OF BAUCHI STATE HOLDS EDUCATION STAKEHOLDERS MEETING THE (SUBEB)