KEEP:SHIRA DA GIADE SUN AMFANA DA WANNAN GAJIYAN SHIRI NA(KAURA ECONOMY EMPORWERMENT PROGRAMME)#KSMF REPORTERS BAUCHI.
A ci gaba da shirin Kaura Economy Empowerment Programme ( KEEP ), wadda a halin yanzu an kammala kananan hukumomi sha biyu, cikin hukuncin Allah yau Gwamna Bala Mohammed ya kaddamar da kananan hukumomin Shira da Giade.
Cikin jawaban mai girma Gwamna, yace ya kirkiri wannan shiri ne don yakan talauci a tsakanin al'umma da bunkasa tattalin arzikin jihar Bauchi, ya kara da cewa Programme din KEEP, akwai rabon motoci, mashina da sauran kayan sana'o'i, don dogaro da kai. Da kuma samar da jari ga kananan yan kasuwa.
Gwamnatin Bala Mohammed ta samar da aiyukan raya birni da karkara, wajen gina tituna, gyara da gina makarantu da asibitoci da dai sauran su.
Gwamna Bala Mohammed yayi gargadi musamman ga shuwagabanni da su guji sayar da filaye dan samun kudin shigan kansu, ya kara da cewa bai dauki harkan tsaro da wasa ba, don haka akwai kyakyawan fahimta tsakanin sa da masarautun gargajiyar, da kuma malaman addinai.
Gwamnatin jihar Bauchi ta cancanci yabo, musamman yadda itace na uku a Nigeria wajen zaman lafiya
Daga karshe yayi alkawarin, samar da tituna tsakanin kanan hukumomi Shira, Giade da Katagum wadda suka hada Zibo-Gagigba-Baili-Dango-Zigau-faggo har zuwa Bukul dake ƙaramar hukumar Katagum.
✍️ Kabiru Dalhatu
Fin. Sec. KSMF and (Baban Zarah)
30th March February