GWAMNAN BAUCHI BALA YANA CIGABA DA INGANTA FANNIN LAFIYA A JIHAR BAUCHI!#KSMF REPORTERS BAUCHI....
#KSMF Gwamnatin Jihar Bauchi Tayi Nisa Wajen Inganta Kiwon Lafiya a Jiha, Da Yawan Mutanen Mu Basu San Da Wannan Ba.
Wannan Ma'aikata Ce Ta Musamman Na Kula Da Kiwon Lafiya Da Gwamnatin Ƙauran Bauchi Ta Ƙirƙiro Musu Matsuguni Na Dindindin Saɓanin Cigaba Da Zama a Takure a Gun Haya, Wanda Suka Shafe Shekara Da Shekaru.
Kamar Yanda Kuke Gani a Hoton Nan Wannan Gini Na Kan Hanyar Ajiya Adamu Road, a Tsohon Gidan Marigqyi Amb. Balarabe AKA (Balabasa). Dake Gundumar Mu Dawaki Ward Bauchi.
Akwai Maka Makan Ɗakunan Taron Ma'akata, Ofisoshi, Gurin Bayi, Ko Wani Sashi Beni Ne Akwai Sassa Guda Shida Harda Ɗakunan Masu Gadi.
Yanzu Haka Aiki Ya Kusan Zuwa Ƙarshe Domin Aikin Yayi Nisa Wasu Guraren Fenti Kawai Suke Jira, Muna Ci-gaba Da Fatan Alhairi Wa Gwamnatin Jihar Bauchi Allah Idda Nufin Alhairi.