AN GUDANAR DA MUSABAKAN KARATUN ALQUR'ANI MAI GIRMA A JIHAR BAUCHI KARO NA 36 KUMA JIHOHI 36 SUKA HALARTA MAI GIRMA GWAMNA YA KAWATA WANNAN MUSABAQA YADDA GWAMNATINSA TA BADA TALLAFI KUDI NA 100,000,000,00! #KSMF REPORTERS BAUCHI,

Gomnan jihar Bauchi yabayyana bada Tallafin karatu wa Yarinya yar' Shekara Biyar Yar' Asalin jihar Cross Rivers

: Yabada tallafin Naira Miliyan 25 wa wadda sukayi Nasara, Wadda suka halarta, da Alkalai na Musabaka

Gomna Bala Muhammad Abdulkadir na jihar Bauchi a ranar Asabar yabayyana bada tallafin Karo karatu wa yarinya yar' Shekara Biyar mai Suna Amina Idris Muhammad daga jihar Cross Rivers, Wadda itace yar' karama a duka cikin wadda suka halarci musabakar Karo na 36 wadda yagudana a jihar .

Gomnan yabayanna hakane a lokacin rufe gasar wadda yagudana a filin wasanni na tunawa da Sir Abubakar tafawa Balewa, Wannan Abu yabiyo bayan irin kokari da tayi na wajen karatun Qur'ani.

Gomna Bala Muhammad Abdulkadir yace wannan bakaramin dama bace a Gomantinsa na karban bakwancin mahaddata Qur'ani Mai tsarki a jihar Bauchi, Sannan Shine abunda duk wani musulmi ke tinkaho dashi a duniyanan.

Yace Musabakar al'qurani bawai kawai Azo ayi bane abada kyaututtuka, yace nada kyau ayi hadda akuma kiyaye dukkan ka'idodi da ayoyi na littafi Mai tsarki a Kuma yi anfani dashi ta yadda Allah yace.

"Kwanaki Tara da aka Shafe ana fafatawa a tsakanin mahalarta Gasar, Ansamu da kuma nuna ingantaccen Gogewa, kwarewa wajen baje ayoyi da karantasu wadda Qur'ani shine kadai littafin da miliyoyin mutane suke haddaceshi  a duniya baki daya'.

" Gomnatin jihar Bauchi, bazata gajiyaba wajen taimakon wannan gagarumin aiki ba, Ina Mai bayyana muku cewa nabada kyautan Naira Miliyan 10 wa Wadda sukayi Nasara, Naira Miliyan 10 wa Wadda aka fafata dasu, Naira Miliyan 5 wa alkalai.

" In zaku tuna tun lokacin da aka Fara musabaka na al'qur'ani Shekarar 1985, Wannan shine Karo na Uku da jihar Bauchi takarbi bakwancin musabaka, Gashi a yanzu a zamanina anyi, Samun damar haddace Qur'ani zallah batare da Gwaji ba akullun ana samun koma baya.

Gomnan yayi anfani da wannan damar yayi Kira ga Malaman Addini Shuwagabannin al'ummah dasu yi dukkan Mai yuyuwa wajen ganin ansamu tagari Nan gaba don Basu tarbiyya na yadda yadace.

" Anamu banagren na Shuwagabanni, dole muji tsoron Allah, baxaiyi taba yuyuwa ba bamuyi abunda yakamata ba muce dole mabiyanmu suyi abunda yadace Lura da yadda ake fuskan tar matsala akasa, Dole muyi addu'a muroki Allah a kowani lokaci da yakaremu da kariyansa.

Anasa jawabin Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar yayi Kira ga Shuwagabannin addinin Musulunci da masu bincike da su bullo da wani idea daxai sauya yadda ake gudanar da musabakar wajen ganin anyi bunkasa musabakar Quranin don habaka addinin Musulunci da samun zaman lafiya mai dorewa.

" Wannnan babba Kuma muhimmin abune da kowa yataimaka wajen ganin yan'baya sun anfana da Karatun da Kuma karantawa, yabukaci kowa da kowa dasu bada nasu gudumawa don cigaba da dabbaka Qur'ani

Ofishin babban Mai bada shawara wa Maigirma Gomna kan yada'labarai  Comrade Mukhtar Gidado mnipr

Popular posts from this blog

UNMASKING OMOYELE SOWORE'S HIDDEN AGENDA- BY SENIOR SPECIAL ASSISTANT FOR GOVEDNOR OFFI CE HON.SULEIMAN MUSA MAI POSTER

GOVERNMENT OF BAUCHI STATE HOLDS EDUCATION STAKEHOLDERS MEETING THE (SUBEB)