GWAMNAN JIHAR BAUCHI BALA YA DAWO DA JIHAR BAUCHI CIKIN HAYYACINTA!#KSMF REPORTERS BAUCHI....
Shekaru sha biyu da suka gabata jihar Bauchi bata cikin jihohin da ake kwatancen su a ayukan cigaba na mulkin Demokradiyya ta farnin hanyoyi, ilimi samar da gidaje da inganta harkan lafiya da sauran wasu fangarori wanda ba sai mun ambacesu ba amma kowa yasan an yisu a Jihar Bauchi.
Wanda har an kai matsayin da aka fara kwatanta cigaban jihar Gombe da Bauchi wanda hakan abun kunya ne a gare mu, saboda mu iyayen su ne,
Hakan ya faru ne na rashin samun shugabanni masu kishin jihar su, hakan yasa wasu jihohin da suke bayan mu suka zo suna goga kafa da mu..
ALHAMDULILLAH
Zuwan sen BALA ABDULKADIR KAURAN BAUCHI a matsayin gwamnan jihar Bauchi, ya kawo mana cigaba masu tarin yawa, ta fannoni masu yawan gaske wanda yanzu jihar Bauchi tana cikin jihohin Najeriya wanda suke samu romon Demokradiyya, ta farnin samar da hanyoyi a fadin jihar Bauchi, gyaran asibitotin jihar Bauchi wanda a baya akayi watsi da gyaran su,
Suma sarakunan gargajiya a jihar Bauchi baa barsu a baya ba, an gyara masu fadodinsu an samar masu da motocin hawa,
Saboda haka indai cigaban jihar Bauchi mu keso yakamata mu sake ba da dama wa KAURAN bauchi a zaben 2023 don cigaba da ayukan alheri a jihar Bauchi 🙏 🙏