GWAMNAN JIHAR BAUCHI SANATA BALA ZAI GINA HANYOYI MASU TSAWON KILO MITA DARI BIYU (200)!#KSMF REPORTERS BAUCHI...

Gwamna Bala Abdulqadir Mohammed na Jihar Bauchi zai gina hanyoyi masu tsawon kilo Mita Dari biyu (200).

Mai girma Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulqadir Mohammed zai gina hanyoyin mota mai tsawon kilo Mita Dari biyu a yankunan karkara na Jihar.

Hanyoyin sun hada hanyar Miya zuwa Soro a Karamar Hukumar Ganjuwa, Rishi zuwa Tama a Karamar Hukumar Toro, Rimin-Zayam zuwa Polchi wadda ya hada Kananan Hukumomin Toro da Dass sai kuma Misau zuwa Miya wadda ya hada Karamar Hukumar Misau zuwa Karamar Hukumar Ganjuwa.

Sauran ayyukan hanyoyin sun hada hanyar Mararaban Liman Katagum, Hanyar Yashi zuwa Guguri da kuma hanyoyi a cikin garin Azare helkwatar Karamar Hukumar Katagum.

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Alhaji Abdulkadir Ibrahim Kwamishinan ayyuka na Jihar Bauchi.

Popular posts from this blog

UNMASKING OMOYELE SOWORE'S HIDDEN AGENDA- BY SENIOR SPECIAL ASSISTANT FOR GOVEDNOR OFFI CE HON.SULEIMAN MUSA MAI POSTER

GOVERNMENT OF BAUCHI STATE HOLDS EDUCATION STAKEHOLDERS MEETING THE (SUBEB)