AIKIN TITIN CENTRAL MARKET ZUWA MAKERA,MAI GIRMA GWAMNA SANATA BALA KAURA MAI FADA DA CIKAWA!#KSMF REPORTERS BAUCHI.
Alhamdulillahi,masha Allahu muna kara godiya ma Allah da kuma Shugabanmu.
Aikin titin data tashi daga shakatafi na kasuwan central market zuwa kan titin makera komai yana tafiya dai dai. Tuni wannan hanya an daura masa kwalta.
Wannan hanya Gagara ba daune domin tun lokacin Gwamna Ahmad Adamu Mu'azu ake fada da baki cewa za'ayi wannan hanya.
Amma cikin hukun Allah da zuwan Dan'gari Mai kishin Gari kuma wanda yasan gari da mutanen Gari. Mai Girma Gwamna Sanata Bala ya bada Umarnin yin wannan Hanya a cikin watanni kalilan kuma gashi yadda aikin ya kasan kowa zai iya bin wannan hanya.
Kamar yadda Mai Girma Gwamna Bala yayi alkawarin sabunta Garin Jihar Bauchi a lokacin da yake neman kuri'a a Jihar Bauchi babu abunda zamu fada sai muce kwalliya ta biya kudin Sabulu.
Daga Karshe muna Godiya ma Ubangiji daya bamu mai kishinmu wanda yasan damuwarmu kuma ya share mana damuwar a lokacin daya dace. Hakanne yasa mutanen Jihar Bauchi suke masa fatan Alheri.
Mungode: KAURA GO FOR 8.